Tsarin Manhajar ANDROID
=======================
Manufar Gina Android
=======================
Manufar Gina Android
A karo na uku, Kungiyar OHA (Open Handset Alliance) ta sake lura da su
kansu nau’ukan masarrafan da ake loda wa wayoyin salula, sai ta ga su ma
suna da alhaki wajen janye wa wayar salula makamashinta na batir. Kenan
ashe ba tsantsar aikin gangar-jikin wayar bane kadai ke cinye batirin,
har da masarrafan da mai waya ke loda su. Wannan ya sa Kungiyar ta samar
da ka’idojin gina manhajojin dake aiki a kan babbar manhajar Android.
Wadannan ka’idoji ta samar dasu ne ta hanyar tsarin Application
Programming Interface (API), wanda tsari ne da duk wani mai son gina
masarrafar da za ta yi aiki a kan babbar manhajar Android, dole sai ya
kintsa su cikin dabarun da yake amfani dasu wajen gina masarrafar,
sannan za a iya aiki da ita a kan babbar manhajar Android.
Wadannan tsare-tsare dai kalmomi ne, ko hadakar kalmomi na yaren kwamfuta, wadanda suka kebanci Android. Ilimi ne mai zurfi, ya jama’a. Asali, galibin masarrafan dake Cibiyar Play Store an gina su ne da dabarun gina manhajar kwamfuta mai suna JAVA. Ita kuma babbar manhajar Android asalinta daga dabarun gina manhajar kwamfuta mai suna C ne da C++. Kenan ashe dabaru ne mabanbanta. Idan kana bukatar tsara maballin da mai mu’amala da wayar salula zai latsa don aiwatar da wani aiki, dole ne kayi amfani da yaren da babbar manhajar Android ke iya fahimta, wanda kuma musamman aka samar dashi don yin hakan, ka cakuda shi da na JAVA, sannan ta fahimci yaren. Nan gaba akwai bayani dake tafe kan wadannan ka’idoji da tsare-tsare. Abin nufi dai shi ne, manufar masu babbar manhajar Android shi ne samar da masarrafan da za su zama masu karancin cin makamashi a yayin da ake aiki dasu a kan babbar manhajar.
Manufa ta karshe, Kungiyar OHA ta sake kallon wayoyin salula don nazarinsu, sai ta tarar akwai matsala da masu gina masarrafai ke cin karo da ita tsakanin wayoyin salula na kamfanoni daban-daban, da kuma nau’i da kintsin shafukan wayoyin. Abin nufi, idan kana son gina manhajar wayar salula, dole a baya sai ka haddade nau’in wayar da za ta iya amfani da manhajar, da kuma girman fuskanta (Screen Siz and Orientation). Kenan ashe idan kana son gina masarrafan da kowace waya mai dauke da babbar manhaja iri daya za ta iya amfani da ita, dole sai ka gina masarrafai iya yawan nau’ukan wayoyin da kake so su iya amfani da ita. Da Kungiyar OHA ta lura da haka, sai tace akwai matsala. Nan take ta tsara hanyoyin da masu gina masarrafar wayar salula (Mobile Phone Developers) za su iya amfani dasu don gina manhaja guda daya tak, wacce za a iya amfani da ita kan kowace irin waya ce, na kowane irin kamfanin waya, mai karamin fuska ce ko babba, in dai tana amfani da babbar manhajar Android. Tirkashi! Wannan manufa na cikin manufofin da suka kara wa babbar manhajar Android shahara, da tunbatsa, da kuma saurin yaduwa a duniya.
zan ci gaba in sha Allah.
Mz Computers Panshekara

Weldon
ReplyDeleteKa kyauta, ya karatu kuma?
ReplyDeleteAlhamdulillah Mal. Haruna Ya aikin
Delete