Tsarin Manhajar ANDROID ======================= Manufar Gina Android A karo na uku, Kungiyar OHA (Open Handset Alliance) ta sake lura da su kansu nau’ukan masarrafan da ake loda wa wayoyin salula, sai ta ga su ma suna da alhaki wajen janye wa wayar salula makamashinta na batir. Kenan ashe ba tsantsar aikin gangar-jikin wayar bane kadai ke cinye batirin, har da masarrafan da mai waya ke loda su. Wannan ya sa Kungiyar ta samar da ka’idojin gina manhajojin dake aiki a kan babbar manhajar Android. Wadannan ka’idoji ta samar dasu ne ta hanyar tsarin Application Programming Interface (API), wanda tsari ne da duk wani mai son gina masarrafar da za ta yi aiki a kan babbar manhajar Android, dole sai ya kintsa su cikin dabarun da yake amfani dasu wajen gina masarrafar, sannan za a iya aiki da ita a kan babbar manhajar Android. Wadannan tsare-tsare dai kalmomi ne, ko hadakar kalmomi na yaren kwamfuta, wadanda suka kebanci Android. Ilimi ne mai zurfi, ya jama’a. Asali, galibin...
Comments
Post a Comment